Paparoma Na Cocin Catholica Ya Yi Tir Da Abinda Yahudawa Sake A Gaza

Paparoma Leo na 14 a jawabinsa na farko a bikin haihuwar annabi Isa (a) ko kirsimeti ya nuna damuwarsa da abinda ke faruwa da palasdinawa

Paparoma Leo na 14 a jawabinsa na farko a bikin haihuwar annabi Isa (a) ko kirsimeti ya nuna damuwarsa da abinda ke faruwa da palasdinawa a Gaza, musamman iyaye da kananan yaransu wadanda basu da abinci ko wurin kwana mai basa samun kulan da ta dace da su a matsayin mutane.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Paparoman yana fadar haka a jiya Alhamis a cikin jawabinsa na farko a kirsimeti tun bayan zabensa a matsayin paparoman Catholica. Kafin haka a jawabinsa na farko bayan zabensa a matsayin paparoma ya kawo maganar abinda yake faruwa a Gaza ya kuma nuna damuwarsa da rashin mutuncin da ke faruwa a yankin. Sannan a lokacin, ya bukaci a kawo karshen yakin a kuma gaggauta shigo da kayakin abinci da bukatun yau da kullum zuwa Gaza.

Paparoman ya kara da cewa”A daren yau, a dai dai lokacinda muke bukukuwan haihuwar shugaban zaman lafiya a garin Bethlaham’ amma zukatammu suna jin nauyin abinda ke irin kukanda iyaye mata da yayansu suke yi a gaza, iyaye wadanda basa cikin aminci, basa da abinci, basa da magunguna sannan basu da fatan zasu fita daga halin da suke ciki.’. Paparoma Leo na 14 ya fadi hakan, muryarsa na rawa sabo girman abinda yake ji a cikin zuciyarsa dangane da abinda ke faruwa a Gaza.  Yayi tir da halin da ake ciki a gaza, ya kuma bayyana shi a matsayin ‘annoba kuma abin kunya ga bil’adama’.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted