Paparoma ya yi kira da a mutunta addinai a Syria

A cikin wani sako, Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, ya yi kira ga dukkan addinai a Syria da su nuna mutunta juna.

A cikin wani sako, Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, ya yi kira ga dukkan addinai a Syria da su nuna mutunta juna.

A rahoton jaridar  al-Quds al-Arabi, Fafaroma Francis ya yi kira da a mutunta juna a tsakanin dukkanin mabiya addinai a kasar Syria, kwanaki uku bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a hannun ‘yan adawa masu dauke da makamai.

A yayin jawabinsa na mako-mako a hedkwatar Vatican, ya bayyana fatan al’ummar Siriya za su zauna cikin koshin lafiya a wannan kasa, kuma addinai daban-daban za su yi aiki tare da gaskiya da mutunta juna domin samun alheri ga mutanen kasar baki daya.

Paparoma ya kuma yi kira da a samar da mafita ta siyasa domin karfafa zaman lafiya da tabbatar da hadin kai a Siriya da kaucewa rikici da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar wannan kasa.

Ya kuma bukaci ‘yan adawa masu dauke da makamai da suka kwace iko da kasar, da su  bi hanyoyi na lumana da  kwanciyar hankali wajen gudanar da mulki ta yadda za a samar da hadin kan kasa. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments