Paparoma Ya Bayyana Hare-haren Da Isra’ila Take Kai Wa Gaza Da Halin Keta

Shugaban Majami’ar Roman Katolika ta duniya Paparoma Francis ya yi tir da hare-haren da sojojin Isra’ila suke kai wa yankin Gaza tare da bayyana shi

Shugaban Majami’ar Roman Katolika ta duniya Paparoma Francis ya yi tir da hare-haren da sojojin Isra’ila suke kai wa yankin Gaza tare da bayyana shi a matsayin keta.

Shugaban majami’ar roman katolina ta duniya wanda ya gabatar da jawabi a jiya Asabar  ya kara da cewa; “A jiya an kai wa kananan yara hare-hare da bama-bamai, wannan halayya ce ta keta. Wannan ba yaki ba ne. Na fadi haka ne saboda lamari ne mai kona zuciya.”

Ba kasafai shugaban majami’ar roman katolika din yake daukar banagre a cikin rikice-rikice ba, sai dai dangane da Gaza, ya sha fitowa yana yin Allawadai da hare-haren da HKI take kai wa Falasdinawa,musamman a Gaza.

A wani littafi da aka buga a watan da ya shude, shugaban majami’ar roman katolikan ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa kisan kiyashi ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments