Pakistan Za Ta Sayar Wa Da Libya Makamai Na Dala Biliyan 4

Kashashen na Pakistan da Libya sun cimma yarjejeniya akan cinikin makamai na dalar Amurka biliyan 4 duk da cewa MDD ta haramta a sarya wa

Kashashen na Pakistan da Libya sun cimma yarjejeniya akan cinikin makamai na dalar Amurka biliyan 4 duk da cewa MDD ta haramta a sarya wa da Libya makamai.

Wasu jami’an gwamnatin kasar Pakistan sun saanr da cewa kasashen sun cimma wannan yarjejeniyar ne wacce ita ce mafi girma a tarihin kasar Pakistan.

An cimma wannan yarjejeniyar ne dai a tsakanin babban hafsan hafsoshin sojan kasar Pakistan Janar Asim Munir da kuma Saddam Halifa Haftar a makon da ya wuce a birnin Banigazi na kasar Libya.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” wanda ya ga takardar yarjejeniyar ya ce, ta kunshi jiragen yaki 16 samfurin “JF-17” da aka kera su ta hadin gwiwa a tsakanin Pakistan da China. Sai kuma Wasu jiragen 12 da ake amfani da su domin bai wa matuka horo.

Wani jami’in Pakistan ya kuma ce; daga cikin makaman dake karkashin yarjejeniyar da akwai na ruwa,kasa da kuma sama. Jami’in ya kuma ce, kudin makama da Pakistan za ta sayar wa da Libya din za su kai dala biliyan 4.6.

Tashar talabijin din kasar Libya ta byar da labari a jiya Lahadi cewa,bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar aiki tare ta fuskar tsaro daga ciki har da bayar da horon soja, da kuma kera makamai ta hanyar hadin gwiwa.

 Kasar Libya dai tana fuskantar takunkumin MDD tun a 2011 da yah ana a kai ma ta makamai ko wasu abubuwa da za a iya sarrafa su, su zama makami.

Ya zuwa yanzu babu tabbacin ko daya daga cikin wadannan kasashen sun gabatar da bukata ga MDD akan ta yi togiya akan wannan cinikin makaman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted