Najeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda

Gwamnatin Najeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyi masu daukar makamai a matsayin ’yan ta’adda. An dau wannan matakin ne a wani sabon mataki mai manufar kara tsaurara yaki da sace-sacen mutane da hare-hare da kuma tashin hankali musamman a yankunan karkara. Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a taron […]

Gaza: Falasdinawa 410 aka kashe tun bayan cimma yarjejeniya

Hukumomin Gaza sun ce fiye da Falasdinawa 410 ne aka kashe, wasu 1,112 kuma suka jikkata a hare-haren Isra’ila a Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ba da rahoton cewa, laifuka 875 Isra’ila ta aikata a yarjejeniyar, ciki har […]

Iran na shirin harba tauraronta mafi girma a ranar 28 ga Disamba

Iran na shirin harba wani tauraron dan adam da bata taba yin irinsa ba zuwa sararin samaniya a karshen watan Disamba a matsayin wani bangare na kokarinta na fadada ayyukanta na sararin samaniya. A cewar rahotannin da kafofin watsa labarai na cikin gida suka wallafa a, za a harba tauraron dan adam na Paya da […]

Pakistan Za Ta Sayar Wa Da Libya Makamai Na Dala Biliyan 4

Kashashen na Pakistan da Libya sun cimma yarjejeniya akan cinikin makamai na dalar Amurka biliyan 4 duk da cewa MDD ta haramta a sarya wa da Libya makamai. Wasu jami’an gwamnatin kasar Pakistan sun saanr da cewa kasashen sun cimma wannan yarjejeniyar ne wacce ita ce mafi girma a tarihin kasar Pakistan. An cimma wannan […]

Venezuela Ta Bukaci Amurka Ta Kawo Karshen Aikin Soje A Ruwayen Yankin Carebian

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Yvan Gil yayi kira ga gwamnatin kasar Amurka ta kawo karshen jibge sojoji a ruwayen yankin Carebian, da kuma takunkuman da basa bisa ka’idan da ta dorawa kasar Venezuela. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gil yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa, […]

HKI Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Birnin Qudus

Motocin Buldoz na HKI sun rusa gidajen Falasdinawa a tsakiyar birnin Qudus a jiya Litinin, inda suka bar iyalan Falasdinawa 13 suka rasa inda zasu sa kansu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ta bayyana cewa hakan ya awku ne a unguwar  Wadi Qaddum, inda suka ci mutuncin falasdinawa mata da dama kafin su […]