Pakistan: Za Mu Ci Gaba Da Kasuwanci Da Iran Ba Tare Da La’akari Da Takunkumin Amurka Ba

Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta sanar da cewa za ta ci gaba da mu'amalar kasuwanci da Iran domin takunkumin Amurka nata ne ita kadai.

Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta sanar da cewa za ta ci gaba da mu’amalar kasuwanci da Iran domin takunkumin Amurka nata ne ita kadai.

Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta kuma ce; Pakistan kasa ce mai aiki da dokokin kasa da kasa,kuma takunkumin da aka kakaba wa Iran ba daga MDD ya fito ba.

Pakistan din ta kuma ce; a halin yanzu tana aiki tare da bangarorin Iran da Amurka domin ganin an warware sabani a tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da diplomasiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted