Pakistan Ta Gayyaci Wakilin Amurka Kan Batun Yankin Kashmir

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Pakistan ta kira babban jami’in diflomasiyan Amurka da dake Islamabad  domin nuna rashin amincewa da bayanan da jakadan Amurka yayi

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Pakistan ta kira babban jami’in diflomasiyan Amurka da dake Islamabad  domin nuna rashin amincewa da bayanan da jakadan Amurka yayi a kasar Indiya game da batun rikicin yankin Kashmir

A cikin bayanin da ta fitar a jiya laraba maaikatar harkokin wajen kasar Pakistan tace ta gayyaci babban jami’in dake kula da harkokin Amurka a Islamabad Natalia Baker, game da babbar takaddamar da aka shiga kan kalaman da basu dace ba da jakadan Amurka Sargio gor yayi a kasar Indiya

Pakistan tayi All.. wadai da kakkausar murya, kuma tayi watsi da matsayin Jammu da Kashmir a matsayin wani bangare na indiya inji ma’aikatar harkokin wajen Pakistan, yace jamu da Kashmir  an san sabanin dake tsakaninsu a mataki na kasa da kasa, kuma ana jiran matakin karshe da zaa dauka ne da yayi daidai da kudurin majalisar dinkin duniya kan abin da ya shafi mutane Kashmir

Gwamnatin Indiya da fira ministan indiya ke jagoranta Narendra Modi ya soke batun yancin kan yankin Kashmir tun a shekara ta 2019 a watani mataki da kasar Pakistan ta kirashi da wanda ya sabama doka sai dai kotun indiya ta dakatar da shirin a shekara ta 2025

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted