Gwamnatin shugaba Trump tana matsawa gwamnatin kasar China ta taimaka mata wajen dorawa Iran takunkuman tattalin arziki mafu muni da ta dorawa JMI don durkusar da ita. Amma gwamnatin Beijin tana jada baya, tare da cewa a ganint takunkuman tattalin arziki ko yaki ba zai taba amfani ko ya warware matsalar Amurka da Iran ba.
Wannan matakin da kasar china ta dauka ya zo dais aura makon guda Xi Jinping shugaban kasar China ya gana da Donal Trump a fadar white House.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto gwamnatin kasar ta China na fadar haka a yau Jumma’a kuma ta kara da cewa, maida Iran saniyar ware a bangaren tattalin arziko da kuma takura mat aba zai taba warware matsalolin da ake fuskanta a yankin yammacin Asiya ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Lin Jian ya yi kira ga Washington da ta koma kan turbar tattaunawa da diblomasiyya ta neman hanayar warware matsalolinta da Tehran. Ya sake nanatawa takunkuman tattalin arziki da takurawa Iran ba zai taba magance matsalolin yankin ba. Lian ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa, shawarar kasar China it ace bangarorin biyu su koma kan teburin tattaunawa.
Kafin haka sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya bada sanarwan dorawa Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, sannan ya ja kunnen sauran kasashen duniya kan sabawa takunkuman na Amurka, saboda duk wanda ya saba shi ma Amurka zata yi maganinta.
Bessent ya fada a shafinsa na X kan cewa dole ne kasashen duniya su yanke dukkan harkokin tattalin arziki da Tehran ko su gamu da fushin Amurka.