Yansandan najeriya a jihar Kaduna sun ceci mutane 75, wadanda suka hada da mata da yara daga hannun wasu yan fashi dauke da makamai a kusa da garin Folwaya a cikin karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto kakakin yansanda DSP Mansir Hassan yana cewa matafiyan wadanda yan kabilar Fulane ne, sun fada hannun yan fashin ne a ranar 19 ga watan Augusta wato ranar Larba, da misalign karfe 5:30 na yamma.
Yan fashin na dauke da bindigogi shamfurin AK-47 da dama, kuma yansandan sun sami labarin ne daga kungiyar derebobin motocin haya ta kasa (NURTW) reshen birnin Gwari.
Yan fashin sun boye mutanen ne a wani kogo tsakanin wasu duwatsu a kusa da inda suka sacesu.
Daga karshe yan fashin sun gudu bayan da suka ga yansanda sun isa wurin da motocinsu da kuma kayakin aiki masu yawa. A nan ne suka nemi inda suka boye mutanen suka kuma cecesu ba tare da wani daga an jikata wani ko rasa rai ba.
Kwamishinan yansanda na Jihar Kaduna CP Rabiu Mohammad ya yabawa kungiyar direbobin haya na birnin gwari wadanda suka bawa yansanda labara a cikin lokaci, wanda ya kai ga ceton mutanen.