Babban hafsan sojojin kasar Iran ya gargadi makiya kan kuskuren lissafi, idan sun sake farwa kasar da yaki.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Ali Abdullahi, babban hafsan hafsoshin sojojin JMI yana fadar haka a lokacin zagayowar ranar masana’antun kayakin yaki na kasar Iran wato ranar 22 ga watan Augusta na ko wace shekara.
Ya kuma kara da cewa JMI tana samun ci gaba sosai a nau’I da kuma karfin makamanta. Ya ce, masana’antun makaman kasar suna sabonda dukkan makaman da suka kwana biyu saboda tafiyar da sabbin ci gaban da ake samu na ilmi da fasahar zamani.
Yace: Ina sake nanatawa, sojojin kasar Iran suna kara samun wayewa a fannonin yaki daban daban. Kuma haka al-amarin yake a dukkan bangarorin sojojin kasar, na kasa. Sama da ruwa, na cyber da kuma sararin samaniya. Wanda zai tafi dai dai da duk wani kuskuren da makiya zasu yi idan sun sake farwa kasar da yaki.