Gawakin shahidai kimani 50 ne aka gudanar da jana’izarsu a jiya Alhamis a gaza, 19 daga cikinsu yara kanana ne.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an zakulo gawakin falasdinawan daga karkashin buraguzan gine gine n da HKI ta rusa a kansu ne bayan shekaru uku da fara kissan kiyashi a gaza. Kafin haka an yi jana’izar wasu shahidan kimani 150 wadanda aka zakulo karkashin buraguzan.
Jazana’ar ta gudana a kusa da asbitin sheaf ta Gaza, bayan an tattara gawakin a cikinsa. Kuma har yanzun akwai gawakin shahidai a karkashin buraguzan gine gine wadanda, ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta ce sun kai nauyin ton miliyon 80. Hakan ya hana zakulo sauran dubban gawakin da suke karkashinsa.
Ya zuwa yanzu dai yawan wadanda suke suka yi shahada tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya dara 73,000. Daga cikinsu akwai yara kanana 21,000. Sannan wanu 174,000 suka ji rauni.
Ma’aikatar ta kara da cewa, wata annoba ta bullo a yankin wanda a halin yanzu ya shafi mutane kimani 58,000.