Jaridar Independent ta bayyana cewa: Sojojin Amurka sama da 750 ne suka samu raunuka tun lokacin da suka fara yaki da Iran
Jaridar Independent ta Burtaniya, wacce ta nakalto bayanai daga Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon), ta ruwaito cewa: Adadin sojojin Amurka da suka ji raunuka tun bayan barkewar yaki da Iran a ranar 28 ga Fabrairu ya wuce sojojii 750.
A cewar sabbin alkaluman Pentagon, adadin sojojin Amurka da suka ji raunuka ya kai 757, ban da mutuwar mutane 18 tun bayan fara yakin, tare da samun sabbin raunuka sama da 50 a cikin sabuntawar da ta gabata.
Jaridar ta lura cewa wadannan alkaluman sun zo ne a tsakiyar ci gaba da rikici da takaddama tsakanin Amurka da Iran, yayin da kokarin kawo karshen yakin ya ci gaba da tsayawa.
Alkaluman da suka gabata sun nuna cewa sojojin Amurka 447 ne suka ji raunuka a watan Yuli, kafin adadin ya karu zuwa sama da 750 a cikin sabuntawar da ta gabata.
Wannan sabuntawa ya biyo bayan suka da aka yi wa Pentagon bayan ta cire mutuwar mutane hudu da raunuka da dama daga cikin bayananta na wucin gadi, kafin daga baya ta dawo da su. Ma’aikatar ta danganta canje-canjen da “kuskuren bayanai na wucin gadi.”
Ya kamata a lura cewa Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka, Pentagon, ta riga ta sanar da cewa da gangan ta ɓoye adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka ji raunuka a tsakanin jami’an sojin Amurka da sojoji a yaƙin da suka yi da Iran saboda dalilan “tsaro” da kuma “kare sojojin da aka tura zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.”