Trump Ya Jada Baya Daga Shirinsa Na Karin Kudaden Fito

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jada baya daga shirinsa na kara kudaden fito daga kayakin da suke shigowa Amurka daga mafi yawan kasashen duniya

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jada baya daga shirinsa na kara kudaden fito daga kayakin da suke shigowa Amurka daga mafi yawan kasashen duniya daga ciki har da kayakin abinci.

Kamfanin dillancin labaranTasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, kimani shekara guda da rabi da ya gabata ne shugaba Trump yayi wa Amurkawa alkawalin cewa zai samar da ayyukan yi da dama a kasar ya kuma kyautata tattalin arzikin mutanen kasar tare da dorawa mafi yawan kayakin da suke shigowa Amurka daga mafi yawan kasashen duniya, daga ciki har da wadanda suke fitowa daga kasashe kawayen Amurka.

Amma a halin yanzu saboda hauhawan farashin kayaki a cikin kasar ya dawo daga rakiyar karin kudaden fito, ya rage kudaden fito kan wasu kayakin da ake shigo da su Amurka don rage farashinsu a kasuwa.

 Shugaban ya bayyana haka ne a shafinsa na ‘Trump Social” yana cewa: A yau na tsaida shawara wacce zata rage farashin jan nama ga iyalan Amurkawa masu kwazo.

Kafin haka dai, Trump ya soki shugaban da ya karbi mulki a hannusnu, kan yadda ya bar farashin jan nama ya tashi a kasar.

Ya ce idan an shigo da jan nama daga kasar za’a saida su kasha 25% kasa da farashinsa na yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted