Pakistan: Rikicin Siyasa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar  Jami’an tsaro  4

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Pakistan ta sanar da cewa a yau Talata Jami’an tsaro 4 sun rasa rayukansu sanadiyyar taho mu gama da

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Pakistan ta sanar da cewa a yau Talata Jami’an tsaro  4 sun rasa rayukansu sanadiyyar taho mu gama da magoya bayan tsohon  Fira ministan kasar Imran Khan.

Sanarwar ta Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Pakistan ta kuma ce, ‘jami’an tsaron sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa magoya bayan Imran Khan da su ka kusta cikin  babban birnin kasar daga yankuna mabanbanta.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa; ‘yan jarida sun ga yadda aka yi taho mu gamar a tsakanin jami’an tsaro da kuma masu Zanga-zangar.  Jamian tsaron sun harba albarusan roba akan magoya bayan Imran Khan.

An kuma yanke hanyar sadarwa ta Internet a cikin yankunan da aka yi taho mu gamar.

Kamfanin dillancin labarun na Faransa ya ambato ‘yan sanda suna cewa; Masu Zanga-zangar  suna da makamai, kuma sun kai farmaki akan ofisoshin ‘yan sanda dake yammacin Islamaabad dake da nisan kilo mita 10 daga wata cibiya ta gwamnati da suke son yin zaman dirshan a gabanta.

A wani bayani da ofishin  Fira ministan kasar Shahbaz Sharif ya fitar, ya ce abinda ya faru ba zanga-zanga ce ta zaman lafiya ba, wuce gona da iri ne.

Magoya bayan Imran Khan sun yi gangami ne zuwa babban birnin kasar, domin yin matsin lamba a sake shi daga inda ake tsare da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments