Pakistan Kai Hari A Cikin Kasar Afghanistan Tare Da Kashe Mutane 28

Gwamnatin kasar Pakistan ta sanar da kai hari a kan cibiyoyin masu dauke da makamai a cikin kasar Afhganistan tare da kashe 28 daga cikinsu
afghanistan

Gwamnatin kasar Pakistan ta sanar da kai hari a kan cibiyoyin masu dauke da makamai a cikin kasar Afhganistan tare da kashe 28 daga cikinsu

Sanarwar ta ce an kai harin ne a wasu sansanoni da suke a yankunan Baktika da Konar, sai dai MDD ta ce an kashe fararen hula 3 da kuma jikkata wasu 4.

Wani jami’in tsaro na kasar Pakistan ya fada wa kafafen watsa labaru cewa;An kai harin ne a yankunan Baktika da Kornar dake gabashin kasar ta Afghanitsan, yayin da ma’aikatar watsa labaru ta kasar ta ce;an rushe wasu sansanoni guda 3 daga ciki har da cibiyar bayar da horo ga masu kai harin kunar bakin wake.

 A can kasar Afghanistan kuwa kakakin gwamnatin kasar Taliban Hamdallah Fitrat ya bayyana cewa; Harin na Saudiyya ya shafi wani gida wanda kuma ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 3 da jikkata wasu 4 a cikinsa.

Dangane da wuraren da aka kai wa hari a gabashin kasar kuwa,kakakin gwamnatin kasar ta Afghanistan ya ce, an rusa wata cibiyar kasuwanci da gidan babu kowa a cikinsa.

Kakakin na gwamnatin Afghanistan Zabihullah Mujahid ya ce; Tabbas kasarsa za ta mayar da martani akan wannan harin na Pakistan.”

Ita kuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Afghanistan ta sanar da kiran babban jami’in diplomasiyyar Pakistan domin gabatar masa da koke akan wannan harin. A ranar juma’ar da ta gabata ne da aka kai wani hari a yankin Kohat dake Arewa maso yammacin Pakistan wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 24.

Har ila yau gwamatin kasar ta Pakistan ta sanar da kashe wasu sojojinta 6 daga cikinsu da akwai jami’ai 2, a wani fada da aka yi akan iyakokin kasashen biyu.

Pakistan dai tana zargin kasar Afghanistan da bayar da mafaka ga masu tsattsauran ra’a yi da suke ketare iyaka suna kai mata hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted