Kungiyar Hadin Kan Islama (OIC) ta yi Allah wadai ta yi Allah wadai da taswirar da Isra’ila ta buga mamaye da yammacin Kogin Jordandawasu muhimman sassan Lebanon, da Siriya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto dga wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta OIC ta fitar a jiya Juma’a, inda ta yi Allah wadai da kiran da Isra’ila ke yi na neman mamaye yammacin gabar kogin Jordan, ta kuma soki jami’an Isra’ila da bayar da shawarar kara kai hare-hare kan zirin Gaza, tare da bayyana wadannan ayyuka a matsayin cin zarafin kasa da kasa.
Kungiyar ta sake jaddada kin amincewa da wadannan munanan dabi’u na Isra’ila, dake ci gaba da kai hare-hare kan Falasdinawa a dukkanin yankunan da aka mamaye.
Kungiyar ta OIC ta yi kira ga kasashen duniya da su sauke nauyin da ke wuyansu na kawo karshen cin zarafin da Isra’ila ke yi da kisan kiyashi da ake yi wa al’ummar Palastinu watanni 15 da suka gabata.
Fitar da taswirar dai ya zo daidai da kalaman ministocin yahudawan masu tsattsauran ra’ayi a gwamnatin Isra’ila da ke karfafa ra’ayin mamaye yammacin kogin Jordan.