Mataimakin shugaban kasar Iran mai kula da harkokin sadarwa da yada labarai ya ce tafiyar da shugaban na Iran zai yi zuwa majalisar dinkin duniya za ta kasance a ranar 23 ga watan Satumba.
Mehdi Tabatabai, mataimakin mai kula da harkokin sadarwa da yada labarai a ofishin shugaban kasar Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Mehr, yayin da yake amsa tambaya game da yiwuwar yin shawarwari da Amurka a birnin New York, ya ce: “Na san dai akwai batun tafiyar, amma a halin yanzu babu wani batu na tattaunawa da Amurka a yayin wannan tafiya.”
Ya kara da cewa: “A cikin yanayi da halin da ake ciki a yanzu, akwai bkatar taka tsantsan kan lamurra da dama.
Mataimakin shugaban kasar kan harkokin sadarwa da yada labarai ya kuma bayyana cewa: “A shekarar da ta gabata, yawan tarurruka da ganawa da shugaban kasar ya yi da shugabannin kasashe da tawagogin kasashen waje a Amurka ba a taba ganin irinta ba idan aka kwatanta da shekaru 14-15 da suka gabata.