Ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), reshen Babban Birnin Tarayya, ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin Abuja daga ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2026.
Kungiyar ta ce matakin ya biyo bayan gazawar Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) wajen warware matsalolin da suka dade suna addabar malamai, ciki har da jinkirin karin matsayi, tsaiko wajen ci gaban aiki da kuma canza wajen aikin wasu daraktocin makarantu.
NLC na buƙatar FCTA ta cire sharadin samun guraben aiki kafin a ɗaukaka matsayin malamai, tare da bai wa malaman da suka cancanci daukaka matsayinsu a 2025 damar rubuta jarabawar tare da waɗanda suka cancanta a 2026.
NLC ta bayyana martanin FCTA kan buƙatunta a matsayin wanda bai gamsar ba. Sannan ta umarci ma’aikata a ofisoshin gwamnati, makarantu, asibitoci da sauran hukumomi da su dakatar da ayyukansu har sai an warware matsalolin.