Nijar ta dakile harin ta’addanci a filin jirgin saman Yamai

Gwamnatin Nijar ta sanar da dakile wani harin ta’addanci a babban filin jirgin sama na kasar a Yamai. Kasar ta jinjinawa dakarunta da takwarorinsu na

Gwamnatin Nijar ta sanar da dakile wani harin ta’addanci a babban filin jirgin sama na kasar a Yamai.

Kasar ta jinjinawa dakarunta da takwarorinsu na Rasha a bisa dakile harin da aka kai wa filin jirgin a cikin daren Laraba .

A wata ziyarar gani da ido da ya kai shugaban kasar Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi Faransa da Ivory Coast da kuma Jamhuriyar Benin da mara baya ga maharani da suka kai harin.

Ma’aikatar tsaron Nijar ta ce an kashe 20 daga cikin maharan, an kuma kama wasu 11, yayin da aka kashe sojojin kasar hudu.

An shafe sa’oi ana jin karar fashewa da kuma musayar harbi a wajen da aka kai harin.

Wata kafar talabijin a kasar ta ce daga cikin wadanda aka kashe harda wani dan kasar Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted