Nijar Da Dakatar Da Watsa Shirye-shiryen BBC Da Kuma Maka Gidan Radiyon Faransa Kotu

Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen rediyo na BBC a tashoshin FM a fadin kasar har na tsawon wata uku.

Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen rediyo na BBC a tashoshin FM a fadin kasar har na tsawon wata uku.

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, jiya Alhamis ta zargi BBC da watsa labaran masu cike da kura-kurai, game da yakin da sojojin kasar kr yi da masu ikirarin jihadi.

A sanarwar da ministan sadarwa na Nijar, Sidi Mohammed Raliou, ya labaren na BBC kan iya kawo tarnaki wajen samar da zaman lafiya a kasar.

A wani matakin na daban da gwamnatin mulkin sojan ta dauka a zaman majalisar ministocin da aka yi jiya, ta kuma kuduri aniyar maka gidan rediyon Faransa (RFI) kotu bisa zargin kafar da neman haddasa fitina tsakanin al’umma da “nufin haifar da kisan kare-dangi.”

Ko a farkon watan Augustan 2023, yan kwanaki bayan juyin mulkin da sojojin suka yi sun dakatar da watsa shirye-shiryen gidan rediyon RFI da Talabijin na France 24 na kasar Faransa bisa zargin neman tayar da zaune tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments