New York Times: An Bayyana Amurka A Matsayin Fatalwa

Wani marubuci dan kasar Amurka kasar Amurka a jaridar ” New York Times”  mai suna Stephen Marche ya bayyana cewa; Amurka ta zama daidai da

Asia Times: Manyan Dalilan Rushewar Tarayyar Soveit Sun Fara Bayyana Ga Amurka

Wani marubuci dan kasar Amurka kasar Amurka a jaridar ” New York Times”  mai suna Stephen Marche ya bayyana cewa; Amurka ta zama daidai da fatalwa a fagen siyasar kasa da kasa, duk da cewa tana karfi amma ba ta iya tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a duniya.

Marubucin ya kuma yi Ishara da yadda ake da sabanin siyasa a cikin kasar Amurka da kuma ci gaban da rashin tabbaci akan inda aka dosa.

Marche ya kuma bayyana yadda sabani a tsakanin Amurka da kawayenta ya yi kamari har ta kai ga suna tunanin nesantarta da zama masu cin gashin kansu.

Marche ya ce barazanar da Trump ya yi na kwace iko da Canada da kuma yankin Greenland da kuma kara kudin fito akan kawaye da yi wa kungiyar Nato karan tsaye, duk sun fusata abokan na Amurka.

Marubucin ya kuma yi Ishara da yadda kasar  Canada ta kulla yarjeniyoyin kasuwanci kusa 100 a cikin kankanen lokaci, yayin da kasashen turai su ka rage dogaransu da kamfanoni Amurka na takanolaji,sai kuma kasashe irin su Belgium da Filland su ka kauracewa kamafanoni masu alaka ilimomi na kwamfuta na Amurka kamar Amazon.

A karshe marubucin ya ce Amurkan tana samun koma baya ne a fagen duniya ba saboda tana da masu gasa da ita ba, sai saboda siyasar ita Amurkan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted