Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye.
A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima suna yi, cewa hakan zai gurgunta damar falasdinawa ta kafa kasa mai cin gashin kai.
Yankin da Isra’ila ke fatan ginawa, mashigi ne a bangaren gabashin birnin Kudus, tsakanin birnin da yankin unguwar Ma’ale Adumim, ana kuma ganin gina shi zai haifar da mummunan tasiri, kasancewar hakan zai raba gabashin birnin Kudus da arewacin gabar kogin Jordan, wanda hakan zai dakile damar samar da dunkulalliyar kasar falasdinawa a nan gaba.
Tun a shekarun 1990 ne aka gabatar da aniyar gudanar da ginin wannan yanaki na El, sai dai an dakatar da aiwatar da shi sakamakon adawa daga Isra’ilawa na gida da mazauna ketare. Daga bisani Netanyahu ya sake farfado da batun a shekarar 2012, tare da sake bijiro da shi gabanin babban zaben kasarsa na shekarar 2020.