Araqchi: Babu Dalilin Jin Tsoron Tattaunawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya […]

Welayati: Abin Kunya Ne Yadda Duniya Ta Yi Shiru Kan Laifukan Isra’ila

Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a […]

Ayatullah Khatami Ya Ja Hankalin Kasashen Larabawa Kan Hare-Haren Isra’ila

Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za […]

Gaza: Falastinawa 48 Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila

Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a. […]

Qatar : shugabannin Isra’ila na kishirwar jefa duniya cikin rikici

Firaiministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani Ya bayyana shugabannin Isra’ila a matsayin masu tsattsauran ra’ayi da ke kishirwar jefa duniya cikin rikici. Al-Thani, ya bayyana hakan ne a birnin New York, inda ya halarci taron gaggawa na kwamitin tsaro kan harin da Isra’ila ta kai Qatar. Qatar ta yi lale marhabun da matakin kwamitin sulhu […]

Guteress ya tattauna da Araghchi kan shirin shurin nukiliyar Iran 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a daren jiya Alhamis da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, inda suka mai da hankali kan shirin nukiliyar Iran da batutuwan da suka shafin yankin. tattaunawar na zuwa ne bayan da Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta […]

Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa

fira ministan isra'ila

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye. A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima […]

Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean

Mataimakiyar shugaban kasar Venezuela Delcy Rodriguez ta  yi gargadi game da shirin Washington na kara ruruta wutar rikicin soji a yankin Latin Amurka, tana mai zargin Amurka da neman sauyi gwamnati a Venezuela da kuma sarrafa albarkatun kasar. Rodriguez ta bayyana cewa “kasancewar sojojin Amurka a yankin Caribbean na nufin aiwatar da sauyin gwamnati a […]

Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Doha babban birnin kasar Qatar, ba tare da ambaton sunan Isra’ila ba. TY kuma jaddada wajabcin daina kai irin wadannan  hare-hare da kuma nuna cikakken goyon baya ga  ga ‘yancin kasar […]

Iran da Tunisiya sun amince da kara fadada alaka a tsakaninsu

Ministan harkokin wajen Tunisiya Mohamed Ali Nafti ya ce kasarsa da Iran sun amince da karfafa hadin gwiwa tare da shirya taron komitin hadin gwiwa, yayin da yake maraba da sabuwar yarjejeniyar da Tehran ta kulla da hukumar IAEA. A cikin rubuce-rubuce uku na X a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Tunisia ya bayyana cewa, […]