Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa zai koma yaki ko da an cimma yarjejeniyar musayar Fursunoni da Falasdinawa
Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, koda kuwa an kammala yarjejeniyar musayar fursunoni.
Kalaman na Netanyahu sun zo ne a yayin wani zaman taron ba da shawara na gwamnatin mamayar Isra’ila, inda ya bukaci samun damar cimma manufofinsa na wuce gona da iri, wanda ya tanadi kawo karshen gwagwarmayar Falasdinawa.
Kafofin yada labaran yahudawan sahayonoiyya sun tabbatar da cewa ministan kudin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya shaidawa iyalan yahudawa da ake tsare da su a zirin Gaza cewa ba zai iya ba da tabbacin dawo da wani fursuna a raye daga Zirin Gaza ba.
Wanda hakan ke tabbatar da cewa, rayuwar wadannan fursunonin ba shi ne abin da Netanyahu da gwamnatinsa ke nema ba.