Netanyahu : Sojojin Isra’ila za su ci gaba da zama a Siriya

Firaministan Isra’ila ya ce sojojin kasar za su ci gaba da zama a “yankin da ake kira “buffer zone” a cikin tsaunukan Golan na Syria

Firaministan Isra’ila ya ce sojojin kasar za su ci gaba da zama a “yankin da ake kira “buffer zone” a cikin tsaunukan Golan na Syria da kasar ta mamaye, bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad, har sai an ga tsarin da sabuwar gwamnatin.

Netanyahu ya bayyana hakan ne akan Dutsen Hermon, wanda aka fi sani da Jabal al-Shaykh na kasar Syria, mai tazarar kilomita 10 daga kan iyaka da tsaunukan Golan.

Ya sake nanata cewa Isra’ila za ta ci gaba da kasancewa a yankin “har sai an samu wani tsari da zai tabbatar da tsaron Isra’ila.”

Da alama dai shi ne karon farko da wani shugaban Isra’ila ya taka kafarsa zuwa cikin kasar Siriya.

Siriya ta shiga rashin tabbas tun bayan da gungun ‘yan adawa masu dauke da makamai suka kifar da mulkin Bashar Al-Assad.

Tun lokacin ne Isra’ila ta kaddamar da hare-hare kan sassa daban daban na Siriya tare da mamaye wasu yankunanta tana mai bayyana hakan da wani mataki na hana masu tsautsauran ra’ayin islama amfanai da manyan makamman Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments