Nato Ta Gargadi Donald Trump Akan Yakin Kasar Ukiraniya

Babban magatakardar kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato Mark Rutte, ya gargadi zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump akan aniyarsa ta tilasta kasar Ukiraniya ta yi

Babban magatakardar kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato Mark Rutte, ya gargadi zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump akan aniyarsa ta tilasta kasar Ukiraniya ta yi sulhu da Rasha.

Mark Rutte wanda jaridar “Financial Times” ta yi hira da shi, ya ce idan har Donald Trump ya tilasta wa Ukiraniya ta yi sulhu da Rasha bisa sharuddan da babu daidaito a cikinsu,  ya kuma zama Rasha ce za ta amfana da su, to ya kwana da sanin cewa zai fuskanci sabbin ‘yan adawa.

Rutte ya kuma kira yi Trump da ya goyi bayan kungiyar ‘yarjejeniyar tsaro ta Nato da kuma kasar Ukiraniya,domin Amurkan ce za ta yi asara idan kasashen da suke adawa da ita su ka karu.

Babban magatakardar kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato ya kuma cigaba da cewa; Idan har tsagaita wutar ba a dora shi akan sharuddan da su ka dace ba, to ba zai yi wa Amurkan dadi ba a ce tana da karin kasashen da suke da sabani da ita.

A lokacin da  Donlad Trump yake yakin neman zabe ya yi alkawalin kawo karshen yakin da ake yi a tsakanin Ukiraniya da Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments