Rahotanni sun bayyana cewa Fira minister isra’ila Benjamin natanyahu ya bukaci amincewar kasar Saudiya ta hanyar shiga tsakanin kasar Amurka na shiga cikin yakin da saudiya ke yi da kasar yamen.
Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta fitar da rahoton cewa Natanyahu yana daukar wasu matakai da kara karfafa dangantaka tsakaninsa da birnin Riyadh, da kuma bude hanya wajen ganin an daidaita dangantaka tsakaninsu a nan gaba.
Sai dai yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohamman bin Salman yaki amincewa da wannan bukata saboda fargabar martanin da jamaa za su ,mayar mara dadi, kuma ba tare da amincewasa a matsayin fira ministan masarautar ba , zai yi wuya isra’ila ta samu izinin shiga yakin.
Kasar saudiya ta sha nanata cewa za ta iya daidaita dangantaka da isra’ila ne kawai bayan an kafa gwamnatin falasdinu mai cin gashin kai, wani abu da natanyaho yayi alkawari zai kiyaye a bayanan da yayi a lokacin yakin neman zabe.