Search
Close this search box.

Nasrallah: Mun Samu Babbar Nasara A Harin Martani Kan Isra’ila

Sakatare-Janar na Hezbollah Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa sun mayar da martani kan Isra’ila dangane da hare-haren da ta kai a yankin kudancin Beirut

Sakatare-Janar na Hezbollah Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa sun mayar da martani kan Isra’ila dangane da hare-haren da ta kai a yankin kudancin Beirut wanda ya yi sanadin shahadar babban kwamanda a kungiyar Fouad Shokor.

Babban makasudin harin na jiya wanda aka kaddamar a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da aka yiwa Fouad Shokor, shi ne tarwatsa cibiyar Glilot ta tsakiya na sashin leken asirin sojan Isra’ila Aman, da kuma Unit 8200 da ke kula da ayyukan leken asiri na yanar gizo, dake kusa da Tel Aviv, da kuma tashar jirgin saman Ein Shemer, in ji Sayyed Hassan Nasrallah.

Yayin da yake bayani kan harin mayar da martanin da Hizbullah ta yi jiya, Sayyid Nasrallah ya yi waiwaye dalla-dalla kan wannan farmaki, tare da karyata ikrarin Isra’ila na dakile dukkanin hare-haren na Hizbullah.

Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa, an zabi sunan Farmakin  Arbaeen ne bisa masaniya da cewa shi ne daidai lokacin da duniya ke tunawa da Arbaeen na Imam Husaini. Ya bayyana cewa an fara kaddamar da farmakin ne bayan Sallar Asuba, bayan da mayakan Hizbullah suka shirya komai, da misalign karfe 5:15 na safe.

Dangane da jinkirin mayar da martani, ya tabbatar da cewa Hizbullah  ta shirya tsaf domin daukar mataki tun kwana guda bayan shahadar Kwamanda Fouad Shokor. Duk da haka, jinkirin ya kasance bisa tsari da kuma dubarun yaki.

Ya jaddada cewa, kafin wannan lokacin Hizbullah said a tantance dukkanin wuraren da za ta kai hari, domin kaucewa kai harin kan fararen hula, a kan haka ne farmakin ya mayar da hankali kawai kan wurare ad suke da alaka da sojoji da sauran wurare na tsaron Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments