Akalla Mutane 50 Ne Su Ka Rasu Sanadiyyar Nutsewar Kwale-Kwale A Jahar Sokoto Dake Arewacin Nigeria

Kamfanin dillancin labarun "Reuters" ya nakalto shedun ganin ido suna cewa; Adadin wadanda su ka rasa rayukan nasu sandiyyar hatsarin na jirgin ruwa sun kai
Kwale-kwale ya nutse da mutane

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto shedun ganin ido suna cewa; Adadin wadanda su ka rasa rayukan nasu sandiyyar hatsarin na jirgin ruwa sun kai 50, da akwai kananan yara 40 a tsakaninsu.

Wani jami’i mai kula da hanyoyin ruwa Abdulkadir Yusuf ya bayyana cewa ya ce lamarin ya ce; tuni na gano da tsamo gawawwakin kananan yara 40.

Shi kuwa dan majalisa mai wakiltar yankin da lamarin ya faru a Jahar Sokoto, Nasiru Adamu ya ce mutanen da suke cikin kwale-kwalen da hatsarin ya faru, shekarunsu suna a tsakanin 10 zuwa 15 ne. Haka nan kuma ya ce an yi nasarar ceto da mutane 16.

Shi kuwa wani tsohon kansila a yankin ga Gorau, Ibrahim Musa ya ce, tun an yi jana’izar mutane  46 da su ka kwanta dama sanadiyyar hatsarin.

Wani mazaunin yankin Sama’ila Garba wanda diyarsa yar shekaru 13 ta rasa ranta, ya ce a lokaci irin wannan na damina mutanen da mafi yawancinsu mata ne da kananan yara suna zuwa gonaki domin yin aiki.

Ana yawan samun hatsari irin wannan na kananan jiragen ruwa da suke kifewa da mazaunansu saboda cunkuso da kuma Rashin amfani da ka’idojin kare yankunan da ake zirga-zirga ta ruwa a cikinsu.

A watan da ya gabata ma dai mutane 25 ne su ka rasa rayukansu a hatsari irin wannan a Jahar Yobe dake arewa maso gabashin kasar ta Nigeria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted