Najeriya : ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Yahya Masussuka

Malamman Musulinci da dama na sukarsa saboda akidarsa ta rashin yarda da hadisan Annabi Muhammad S.A.W

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kisan da wasu ‘yan bindiga sukayi wa Sheikh Yahya Masussuka a gidansa da ke yankin Dutsen-Ma.

Sanarwar da rundinar ‘yan sandan ta fitar ta hannun mai magana da yawunta DSP Abubakar Aliyu ta ce an kashe Sheikh Masussuka ne da kimanin karfe 7:30 na yamma a gidansa da ke karamar hukumar Dutsen-Ma a jihar Katsina.

Sanarwar ta ce “wani harin ’yan bindiga ne ya yi ajalin malamin tare da wani abokinsa Adamu Abubakar”.

’Yan sanda sun ce jim kadan bayan faruwar lamarin ne aka garzaya da malamin da abokinsa zuwa wani asibiti da ke kusa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar mutanen biyu.

Sanarwar ta ce tuni ‘yan sandan yankin suka fara gudanar da bincike domin gano suwa ke da hannu a kisan Malamin na addinin Musulinci.

Rahotannin sun ce kafin kisan nasa, Sheikh Masusuka na daga cikin malaman addinin Musulinci wadanda koyarwasu ke haifar da rarrabuwar kawuna a arewacin Najeriya da kasashe makwafta, wanda har ya sanya a watan Nuwamban 2025 gwamnatin jihar Katsina ta yi sammacin malamin.

Malamman Musulinci da dama na sukarsa saboda akidarsa ta rashin yarda da hadisan Annabi Muhammad S.A.W

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted