Najeriya : Tinubu Ya Gabatarwa Majalisar Dokoki Da Kasafin Kudin 2025

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya gabatarwa da majalsiar dokokin kasar da kasafin kudin kasar na shekarar 2025 mai shirin kamawa. Shugaban ya ce kasafin

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya gabatarwa da majalsiar dokokin kasar da kasafin kudin kasar na shekarar 2025 mai shirin kamawa.

Shugaban ya ce kasafin kudin da ya gabatar wa Majalisar na Naira tiriliyan 47.9 na daya daga cikin hanyoyin farfado da Najeriyar.

Wannan shi ne kasafi na biyu da Tinubu ya gabatar tun bayan hawansa mulki.

Bayan gabatar da kasafin shugaban ya wallafa a shafinsa na X cewa : ‘’kasafin da ya gabatar “Zai bada damar aiwatar da muhimman manufofin da muka bullo da su domin sake fasalin tattalin arzikinmu da bunkasa manyan ayyukan raya kasa da karfafa samar da man fetur da iskar gas da sake farfado da masana’antunmu’’.

Tinubu ya kuma bayyana nasarar da ya ce gwamnatinsa ta samu wajen aiwatar da kasafin kudin 2024.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments