Najeriya ta yi hasashen samun karuwar kashi 4.6 cikin dari na GDP a 2025

Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025,

Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024.

Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya.

A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta bayar da rahoton cewa, jimillar darajar kayayyakin cikin gida wato (GDP) ya karu da kashi 3.84 cikin dari a rubu’i na hudu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a 2023, inda jimillar ta karu daga kashi 3.46 a rubu’i na baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments