rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta bayyana farin cikin ta da yarjejeniyar tsaron da aka kulla tsakanin Jamhuriyar Nijar da Algeria wadda za ta bada damar girke sojojin Algeria a Nijar.
Mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya bayyana matsayin kasar yayin wani taron manyan jami’an tsaron da ya gudana a birnin Abuja.
Ribadu ya ce ganin irin halin da yankin Sahel ke ciki, suna bukatar duk taimakon da suke bukata domin tinkarar matsalar ayyukan ta’adancin da ya addabe su.
Mai baiwa shugaban kasar shawara ya ce ya zama wajibi kasashen Najeriya da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso su hada kan su domin tinkarar matsalar, kamar yadda su ma ƴan ta’adda ke hada kai suna kai hare hare ba tare da la’akari da iyakokin kasa ba.