Gwamnatin kasar Brazil ta sanar da cewa Nijeriya a hukumance, ta shiga cikin jerin abokan huldar kungiyar BRICS.
Brazil, wadda ita ce ke shugabantar kungiyar a 2025, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce: Nijeriya ce kasa ta 9 da ta kulla hulda da kungiyar BRICS bayan Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda da Uzbekistan, kamar dai yadda Gwamnatin Brazil ta wallafa a shafinta.
Sanarwar ta bayyana cewa Nijeriya ta kasance kasa da ke kara karfafa hulda da kasashe masu tasowa a duniya, da kuma sauya salon shugabanci, wanda abu ne da Brazil ke bai wa muhimmanci.
A matsayinta na kasa ta shida mafi yawan al’umma a duniya, kuma mafi yawan al’umma a Afirka, kuma daya daga cikin kasashe mafi karfin tattalin arziki a naihiyar Afirka, Nijeriya tana da manufofin kasashen kungiyar BRICS, kamar yadda sanarwar ta ma’aikatar harkokin wajen Brazil ta sanar.
BRICS, kungiya ce da ta kunshi kasashe 10 da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta kudu, Masar, Habasha, Indonesia, Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa.