Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a kasuwar canjin kudaden kasashen waje sun samar da karin kuɗi na suka Naira Triliyan 15 da biliyan 800 tsakanin watan Yunin shekarar 2023 zuwa Disambar 2025.
Ministan Kudin Najeriya, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake gabatar da bayanan sakamakon sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Sai dai sanarwar ta sake bude wata tsohuwar tambaya da ta dade tana yawo a zukatan al’ummar kasar, tun bayan sanar da cire tallafin mai a shekarar 2023, na cewa wai menene amfani cire tallafin? kuma Ina kudaden ke tafiya, tun da ƴan kasa ba sa gani a kasa?
A karin hasken da ministan ya yi, ya nuna cewa ba zunzurutun kudin har sama da tiriliyan 15 din aka ajiye cikin wani asusu na musamman ba, a’a kudaden na tafiya ne a asusun gwamnatocin jihohi da na tarayya wanda ake yi wa al’umma ayyukan ci gaba da more rayuwa.