Najeriya: Sojoji Dari Da Casa’in Sun Mika Takardun Ajiye Aiki

Akalla sojojin Najeriya 195 sun mika takardun ajiye aiki domin kashin kansu ga Rundunar Sojin Najeriya. Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, Rundunar

Akalla sojojin Najeriya 195 sun mika takardun ajiye aiki domin kashin kansu ga Rundunar Sojin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ba ta bayyana dalilin ajiye aikin sojojin ba, amma wasu majiyoyi sun danganta lamarin da rashin kwarin gwiwa a tsakanin sojoji, sakamon matsin rayuwa a kasar.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce Babban Hafsan Sojin rundunar ya amince da aniyar sojojin ta barin aiki domin kashin kansu.

Nwachukwu ya ce sojojin sun bi ka’ida kuma dokar aikin soji ta tanadi hakan, don haka, za su fara hutun barin aiki daga ranar 1 zuwa 24 ga watan Nuwamba, 2024.

Sanarwar da Birgediya-Janar O.H. Musa ya sanya wa hannu ta ce murabus din sojojin zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan na Nuwamba.

Wachukwu ya bayyana cewa rundunar ta yanke tattara jerin sojojin 195 da za su bar aiki don kashin kansu domin sallamar su a lokaci guda ne saboda ta yi musu kyakkyawan tsari kamar yadda ta saba a tsawon shekaru.

Ya ce hakan ya ba da damar bin dukkan ka’idoji da yin shirye-shiryen biyan su kudadensu na sallama da kuma fara karbar fanshonsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments