Najeriya: Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Wuraren Hako Zinariya

Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda  ruftawar ramin hako ma’adanai.

Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda  ruftawar ramin hako ma’adanai.

Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, an kuma ci gaba da aikin ceto na fito da mutanen har zuwa jiya juma’a.

Wani mazaunin yankin ya ce, an ceto da mutane 13 daga karkashin baraguzai, ana kuma jin cewa da akwai wasu mutane fiye da 100 da suke karkashin kasa.

Wani shaidar ganin ido kuwa cewa ya yi, a tsakanin mutanen da sun kai 100 da ramin ya rufta da su, an iya ceto 15 ne kadai.

A Jahar Zamfara da jahohin dake makwabta da ita a arewacin Nigeria ana hako ma’adanai musamman zinariya ta hanyoyin da su ka saba ka’ida ba kuma tare da aiki da ka’idojin kare rayuwa da lafiya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments