Najeriya da Angola sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa wadda ta tanadi soke takardar biza ga masu rike da fasfo na diflomasiyya da na hukuma, wani mataki da aka yi niyya don saukake tafiye-tafiye na hukuma da kuma zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a gefen taron kungiyar Tarayyar Afirka karo na 39 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ne ya jagoranci tawagar Najeriya, yayin da Ministan Hulda da kasashen Duniya, Tete Antonio, ya wakilci Angola.
M. Tuggar ya ce, “Wannan matakin zai zurfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin kasashen biyu, da kuma samar da damammaki masu faɗi don shirye-shiryen hadin gwiwa”
Ambasada Tete Antonio ya nuna cewa “abin lura cewa, idan aka yi la’akari da alaƙar tarihi da ta kafu da kuma tarihin hadin kai tsakanin Najeriya da Angola, za a iya ɗaukar sanya hannu kan wannan yarjejeniya a matsayin abu mai tarihi.”
Najeriya ta yi ikirarin cewa matakan da ta dauka na soke biza sun nuna gagarumin kokarin diflomasiyya wanda ke wakiltar sauyi zuwa ga bai wa kasashen da ke wajen kasashen ECOWAS damar shiga ba tare da biza ba.
A farkon shekarar 2025, Najeriya da Habasha sun amince da irin wannan yarjejeniyar ga masu dauke da fasfo na diflomasiyya da na hukuma, wanda ke saukake tafiye-tafiye a hukumance a fadin nahiyar.