Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin.

Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa.

Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban.

Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya.

A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini da tarbiya.

Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa tare a miƙa ta’aziyya ga iyalai da ƴanuwan da makusantan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin.

Kwankwaso ya bayyana malamin a matsayin uba, kuma babban malami wanda koyarsa ta zama madubi ga ɗimbin al’umma.

Gwamnonin arewacin Najeriya sun nuna alhinin su bisa rasuwar jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Shiekh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a yau alhamis.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutumin da ya damu da harkokin addinin musulunci, mai son zaman lafiya, da samar da fahimta da juriya tsakanin musulmai da mabiya sauran addinai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments