An yi jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ranar Juma’a.
Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci yi waa malamin sallar jana’iza, kuma an binne shi ne kusa da wasu daga cikin iyalansa da suka rasu a baya.
Sheikh Dahiru wanda jagora ne na darikar Tijjaniyya ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma yana da shekara 100 da yan watanni.
Shehin malamin ya rasu ne a asibitin sojojin sama da ke jihar Bauchi ranar Alhamis bayan gajeriyar jinya.