Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa an ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kubutar dalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja.
“Godiya ga jami’an tsaronmu a ‘yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara,” in ji shi. Sai dai ba yi karin bayani ba kan yadda aka ceto su.
“Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a kasa baki daya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan ke faruwa,” in ji shi.
“Haka nan, ina mai farin ciki cewa an gano 51 daga cikin daliban makarantar Catholic School ta jihar Neja.”
Tun da farko, kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce ɗaliban sun gudu ne daga hannun masu garkuwar tsakanin ranakun Juma’a da Asabar bayan sace su a ranar Alhamis da dare.
Wannan yana daya daga cikin manyan garkuwa da mutane a cikin ‘yan shekarun nan, a yankin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke kai hari akai-akai.