Iran ta sake tir da sabon kudurin da Hukumar (IAEA)

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi Allah wadai da kudurin da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta amince da shi kwanan nan game da shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran. Esmail Baghai ya yi wadannan kalamai ne a matsayin martani ga kudurin da Hukumar Gwamnonin IAEA ta amince da shi, wanda Faransa, […]
Harin Isra’ila ya kashe mutum 5 a Kudancin Beirut

Ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin Isra’ila a Kudancin babban birnin Kasar, inda kuma ta raunata kimanin fararen hula 28. A cewar ofishin Firayim Minista Benjamin Netanyahu, harin an kai shi kan “babban hafsan sojojin Hezbollah,” Ali Tabataba’i, wanda Isra’ila ke zarginsa da “jagorantar ƙarfafawa […]
Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sau 500 cikin kwanaki 44

Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza ya ce Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza da Amurka ta shiga tsakani akalla sau 497 cikin kwanaki 44, inda ta kashe daruruwan Falasdinawa tun lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Ofishin ya ce Isra’ila ce ke da alhakin dukkan tabarbarewar al’amuran […]
Najeriya : An sako mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kwara_Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa an ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara. Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kubutar dalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja. […]
‘Yan Isra’ila na neman a gudanar da bincike kan harin ranar 7 ga Oktoba

A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin ba zata na ranar 7 ga Oktoba da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai. Masu zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun taru, a dandalin Habima da ke […]
An Cimma Yarjejeniya A Karshen Taron Kare Muhalli Na Duniya A Kasar Brazil

Taron na kasar Brazil akan muhalli wanda shi ne karo na 30 ya amince da bayar da tallafin kudade ga kasashe masu karancin kudaden shiga domin fuskantar matsalar dumamar yanayin duniya. Mahalarta taron da su ka fito daga kasashen duniya mabanbanta, wadanda suke fafutukar ganin an shawo kan matsalar da ake fuskanta a duniya ta […]
Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin […]
An Fitar Da Kudurin Bayan Taron Kungiyar G20 Ba Tare Da Halartar Kasar Amurka Ba

Shugabannin kasashen duniya da su ka halarci taron kungiyar G 20 sun amince da kudurin akan hanyoyin bunkasa tattalin arziki, sai dai ba a fitar da da cikakken bayani akan abinda ya kunsa ba. Gwamnatin Donald Trump ta ki halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude jiya a kasar Afirka Ta Kudu, da […]
An Kulla Yarjejeniyar Aikin Soja A Tsakanin Kasashen UAE Da Ethiopia

Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Habasha sun rattaba hannu ne akan yarjejeniyar aikin soja a tsakaninsa a wurin baje kolin jiragen sama na wannan shekara ta 2025 a birnin Dubai. A bangaren Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya wakilce ta shi ne Janar Ibrahim Nasir al-Alawi, wanda wakilin ma’aikatar tsaro ne, sai kuma janar Rashid […]
Pezeshkian: Iran na Allawadai da hare-haren Isra’ila a kan Lebanon

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana adawarsa da duk wani mataki da zai iya kara tada hankali, musamman hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Lebanon, yana mai jaddada “wajibcin janyewar sojojin mamaye.” Wannan ya zo ne a cikin sakon taya murna da Pezeshkian ya aika wa Shugaban Lebanon Joseph Aoun a ranar ‘Yanci, inda […]
Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 161

161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. […]
Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran

Ministan ayyukan leken asiri na kasar Iran Esma’il Khatib ya bayyana cewa Isra’ila na fuskantar ayyukan leken asiri mafi muni a tarihin samauwar haramtacciyar kasar, kuma a halin yanzun Jami’an tsaron HKI da dama suna aikin leken asiriwa wa Iran, musamman bayan da gwamnatin yahudawan ta bada sanarwan kama wani sojan rundunar sama ta kasar […]
An Gabatar Da Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar G20 Duk Tare Da Kauracewar Amurka

Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi. Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana gabatar da jawabi bayan taron […]
Zabebben Magajin Garin Birnin NewYork Ya Nanata Cewa HKI Tana Aikata Kissan Kiyashi A Gaban Trump

Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita […]
Venezuela Ta Gargadi Amurka Kan Shirin Tada Hankali A Kan Iyakokin Kasar

Gwamnatin kasar Venezuela ta gargadi kasar Amurka kan duk wani shirin kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro, a dai-dai lokacin da gwamnatin Trump take bada wani sabon yunkuri nan kusa na ganin ta kwace iko da kasar Venezuela, ta kuma raba Madoro da shugabancin kasar. Kafafen yada labarai da dama sun nakalto manya-manyan Jami’an gwamnatin […]
CAN: Yawan Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ranar Jumma’a Sun Fi 300

A dai-dai lokacinda matsalolin tsaro suke kara tarbarbarewa a arewacin tarayyar Najeriya, kungiyar kiristoci ta kasa wato CAN ta bada sanarwan cewa yawan yaran da aka sace a ranar Jumma’an da ta gabat a makarantar St Mary a unguwar Papiri na karamar hukumar Agwara a jihar Naija ya kai 303. Daga cikin wadanda yan bingida […]