Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa, ‘yan gwgawarmayar suna da karfin da za su iya ‘yantar da kasa, don haka abinda ya kamata a yi, shi ne matsin lamba ga Amurka da abokan gaba ‘yan sahayoniya akan keta hurumin kasar.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Hujjatul Islam Na’im Kassim ya ce; A halin yanzu kasar Lebanon tana fuskantar danniyar Amurka, sai dai tambaya anan ita ce, shin za mu iya hana wannan danniyar, ko mu mika wuya, mu bar kasarmu da a karkashin mamaya?
Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi na zagayowar lokacin kafa cibiyar cibiyar musulunci ta makarantu, ya kara da cewa; Abinda Hizbullah take yi, shi ne kare kai daga harin neman kawar da mu da makiya suke yi.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma yi Ishara da manufar makiya ta kai harin bayanan nan a kan gidajen mutane a garuruwan Ayn-qana da Kafar Tabnit da shi ne tsorata su da sanya su mika wuya, sannan ya kara da cewa; ya zama wajibi mu fuskanci wannan abokin gabar da gwargwadon abinda muke da shi, haka nan kuma ci gaba da nuna kin amincewa ko ba shi abinda yake so.
Haka nan kuma Sheikh Na’im Kassim ya jaddada cewa, ba da gaske ba ne cewa kungiyar Hizbullah ce kadai ake kai wa hari, baki daya kasar Lebanon ake hara, don haka aikin kowa da kowa ne ya fuskanci abokan gaba Isra’ilawa.
Haka nan kuma sheikh Na’im Kassim ya ce, Abinda ake da bukatuwa da shi, shi ne tsayin daka, da kuma aiki daga yadda Hizbullah ta dauki shekaru 42 tana gwgawarmaya da Isra’ila.