Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda Shafin watsa labaru na ” al-Ahad” ya yi hira da shi dangane da zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasarallah da Sayyid Safiyuddin, ya ce; kungiyar ta Hizbullah tana jaddada mubaya’arta akan riko da manufofin gwgawarmaya.
Sheikh Na’im Kassim ya yi Ishara da gagarumin taron jana’izar shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da aka yi da kuma ta Shahid Sayyid Hashimi, wanda ba shi da tamka.
Sheikh Kassim ya kuma kara da cewa; Abinda al’umma su ka gani, yana nuni da yadda gwgawarmaya take da tushen a cikin rayuwar mutanen Lebanon.
Haka nan kuma ya ce, jana’izar ta shahidan tana a matsayin jaddada mubaya’a ne ga tafarkin gwgawarmaya da ci gaba da tafiya akansa, da kuma nuni akan yadda al’umma take riko da ita.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Duk da sadaukarwa mai grima da gwagwarmaya ta yin a sakatarorinta biyu, da sauran ‘yan gwgawarmaya, ba za a taba samun nasarar murkushe ta ba,domin an gina ta ne akan kare gaskiya, kuma wadanda suke gwagwarmaya suna tare da Nasara da kuma shahada.
Da yake Magana akan rayuwarsa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, Sheikh Na’im Kassim ya ce; tun a 1987 ne suke aiki tare a lokacin da Shahidin yake shugaban majalisar shawara ta Hizbullahu, shi kuma Na’im Kassim yana mataimakinsa. Haka nan kuma sun kasance a tare a cikin wannan majalisar a tsawon lokacin shugabancin Sayyid Abbas Musawi na Hizbullah.
Shekih Na’im Kassim ya kuma ce, bayan shahadar Sayyid Abbas Musawi a 1992, sun kasance a tare da Sayyid Hassan Nasrallah na tsawon shekaru 31 suna aiki tare a karkashin tutar Imam Khumaini da kuma Imam Ali Khamnei.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce, shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, wani mukami ne na koli da ya samu, amma shi a wurinsa ya yi rashin dan’uwa da su ka kasance a tare na lokaci mai tsawo, wanda a yake samun mafaka awurinsa,sai dai kuma a matsayin na musulmi ya yi Imani da abinda Allah ya kaddara.