A jawabin da ya yi wanda aka watsa ta talbijin din ‘al-manar” babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Gwgawarmaya za ta cigaba, kuma tana da karfin imanin da zai sa karfinta ya karu.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma yi ishara da yadda gwgawarmaya ta sadaukar dakai wajen kare Lebanon da kuma hana abokan gabar nutsawa cikin kasar, sannan kuma tana cigaba da yin tsayin daka.
A gefe daya babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya yi kira ga gwammatin kasar ta Lebanon da ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da ana yin aiki da tsagaita wutar yaki.
Tun bayan tsagaita wutar yakin a tsakanin Lebanon da HKI a ranar 27 ga watan Nuwamba, Isra’ilan take cigaba da keta tsagaita wuta ta hanyar kai hare-hare daga lokaci zuwa lokaci.
‘yan majalisar dake wakiltar gwagwarmaya sun sha yin gargadin cewa idan har HKI ba ta janye daga wasu yankuna da take ciki ba, bayan cikar kwanaki 60, gwgawarmaya za ta yi mu’amala da ita a matsayin ‘yar mamaya.