Majiyar gwamnatin Syria ta ce, mutumin da ya kai wa sojojin Amurka hari a Syria,ya kuma kashe wasu daga cikinsu,an kore shi daga aiki ne saboda tsattsauran ra’ayinsa kwana daya gabanin abinda ya aikata.
Mutumin ya kai harin ne dai a wani wurin taro na tsaro da ya kunshi sojojin Amurka da na Syria. Harin ya yi sanadin kashe sojojin Amurka biyu, da wani farar huka dan Amurka mai fassara, sai kuma jami’an tsaron Syria biyu.
Rahoton da yake fitowa daga Syria yana nuni da cewa ana gudanar da bincike ko mutumin yana da alaka kai tsaye da kungiyar ta ISIS, ko kuwa ya dauki akidarta ne daga nesa.
Harin dai ya sake nuna yadda ake fama da matsalar tsaro a kasar ta Syria a karkashin sabon shugabanta Ahmad Shar, wanda yake kokarin rike madafan iko bayan kifar da gwamnatin Basshar Asad.