Mutumin Da Ya Kashe Sojan Amurka A kasar Syria Dan Kungiyar ISIS Ne

Majiyar gwamnatin Syria ta ce, mutumin da ya kai wa sojojin Amurka hari a Syria,ya kuma kashe wasu daga cikinsu,an kore shi daga aiki ne saboda tsattsauran ra’ayinsa kwana daya gabanin abinda ya aikata. Mutumin ya kai harin ne dai a wani wurin taro na tsaro da ya kunshi sojojin Amurka da na Syria. Harin […]
Iran Ce Ta 10 A Duniya Wajen Yawan Ma’adanin Alminium

Cibiyar nazari da bincike ta majalisar shawarar musulunci ta Iran ta bayyana cewa; Ma’adanin alminiun yana a matukar muhimmanci saboda amfanin da yake da shi a fagen tattalin arzikin duniya.Shugaban cibiyar Dr. Nagahdari ya fada a yau Litinin cewa; Ma’adanin na alminium yana da matukar muhimmanci, kuma wanda ake da shi a Iran zai […]
Iran: An Kaddamar Da Sabbin Ci Gaba A Fagagen Nukiliya Da Kere-kere

A yau Litinin ne Iran ta yaye kallabin sabbin kere-kere na magunguna da aka yi bisa fasahar Nukiliya, a yayin baje kolin kkere-kere karo na 26 a nan birnin Tehran. A yayin wannan bikin wanda mataimakin shugaban kasar Iran Dr. Muhammad Riza Arif ya halarta, da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa Muhammad Islami, […]
Rasha Ta Kakkabo Jiragen Sama Marasa Matuki 130 Da Ukiraniya Ta Harba Ma Ta A Daren Jiya

A wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar, ta bayyana cewa an kakkabo jiragen saman marasa matuki da Ukiraniya ta harba zuwa yankin Rostov. Rahoton na ma’aikatar tsaron Rasha ya kuma ce, wasu yankunan da aka kai wa hare-haren sun kunshi Kamensk-Shaktinsk da kuma Novoshkhtinsk, sai kuma wasu yankuna 9 na gundumar Rostov. Gwamnan […]
An Yi Gagarumin Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaba Maduro A Venezuela

A yau litinin an gudanar da jerin gwano da gangami a cikin birnin Caracas da sauran gagaruwan kasar Venezuela domin nuna goyon bayan al’ummar kasar ga shugaba Nicholay Maduro da yake fuskantar barazana daga Amurka. Masu zanga-zangar dai sun yi Allawadai da yadda Amurka ta keta hurumin kasar ta hanyar kwace jirgin ruwa na dakon […]
Ƙawancen AES Ya Kafa Bankin Raya Kasashe 3 Da Sojoji Ke Mulki

Ƙawancen AES da ya kunshe kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ya kaddamar da bankin raya kasashen 3 na BIDC dauke da jarin CFA biliyan 500 da nufin habaka tattalin arziki da ci gaban kasashen wadanda dukkaninsu sojoji ke mulki. A karshen makon da ya gabata ne ministocin kudi da tattalin arziƙin kasashen 3 […]
Isra’ila Ta Bada Umarnin Rusa Gidajen Falasdinawa Guda 25 A Yammma Kogin Jodan

Rahotanni sun bayyana cewa isra’ila ta ba wa sojoji umarnin rusa gidajen falasdinawaa guda 25 a sansanin yan gudun hijira dake Nur Shams dake gefen tulkaram a arewacin gabar yammacin kogin jodan, a wani shiri da tel aviv ke yi na fadada gine ginen yahudawa a yankunan falasdinawa ba bisa kaida ba. Gwamnan garin tulkarm […]
Wani Dan Majalisar Amurka Ya Bukaci A Janye Dukkan Sojojin Amurka A Siriya

Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar Amurka Ran paul ya sake kira da a kwashe dukkan sojojin Amurka dake kasar siriya, bayan harin da aka kai wa dakarun sojin Amurka a kusa da garin Palmyra a kasar ta larabawa, Paul ya sake nanata kira ne a jiya lahadi kwana daya bayan da aka tabbatar da […]
Masu Zanga zanga Sun Yi Cincirindo A Gaban Ginin Majalisar Dokokin Birtaniya

Daruruwan masu zanga zanga ne suka taru a gaban majalsiar dokokin birtaniya a birnin London domin nuna damuwarsu game da ci gaba da kisan kare dangin isra’ila a gaza, sun dauki matakin ne domin farkar da duniya kan mawuyancin halin da ake ciki a daidai lokacin da zagayowar haihuwar Annabi Isa ke kara karatowa. Ci […]
Tinubu Ya Bukaci ECOWAS Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Juyin Mulki

Shugaban Ƙasar najeriya Bola Tinubu, ya buKaci shugabannin Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), da su yi tsayin daka wajen hana canza gwamnati ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi gargadin cewa barazanar da ke kara bayyana a yankin na bukatar hadin kai da yin aiki tare. Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin da […]
Velayati: Iran na goyon bayan Hizbullah sosai

Pars Today – Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Harkokin Ƙasashen Duniya ya ce Hizbullah ƙungiya ce mai muhimmanci kuma mai sadaukarwa a sahun gaba na ‘Yan Tawaye. A ranar Lahadi, Seyed Abdullah Safi al-Din, wakilin Hizbullah a Tehran, ya gana kuma ya yi tattaunawa da Ali Akbar Velayati, Mai […]
Araghchi : Babu wata mafita daga wajen yankin da za ta iya magance rikicin yankin

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa babu wani mahaluki da zai iya samar da mafita daga wajen yankin da zata ita magance rikicin yankin. Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a wani taro kan halin da ake ciki a Afghanistan. “Abubuwan da suka faru a yankin a cikin ‘yan shekarun nan sun nuna cewa […]
ECOWAS za ta yi tsayin-daka domin kalubalantar juyin mulkin sojoji

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ta ce zata tashi tsayin daka domin kalubalnatar juyin mulkin sojoji. Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar a wannan karo, ya tunatar da takwarorinsa game da bukatar karfafa wannan kungiyar, wadda yanzu ta kunshi membobi 12, sakamakon ficewar membobinta uku: Mali, […]
Hamas ta ce tana da hakkin daukar fansa kan kisan kwamandanta Raed Saad

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce tana da hakkin daukar fansa kan kisan daya daga cikin kwamandojinta wanda ya yi shahada a wani harin Isra’ila. Babban jami’in Hamas Osama Hamdan ya ce kungiyar tana da hakkin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ‘yan Sahayoniya suka yi, musamman kisan kwamandan Raed Saad. […]
Harin Isra’ila ya kashe mutum 3 a kudancin Lebanon

Sojojin Isra’ila sun kashe akalla mutane uku a kudancin Lebanon a lokacin wasu hare-haren sama daban-daban bayan sun yi barazanar sake ci gaba da kai muggan hare-hare kan kasar. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta fitar ta ce wani “harin makiya ” a yankin Yater, a kudancin kasar, ya kashe mutum […]
Albanese ya goyi bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan harin Sydney

Firaministan Ostiraliya Anthony Albanese ya ce, yana goyon bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan mummunan harin da aka kai a bakin tekun Bondi na Sydney, inda ake bikin ranar Yahudawa ta Hanukkah. “Gwamnati a shirye take ta dauki dukkan matakan da suka dace, wannan ya hada da bukatar karin dokokin mallakar bindiga,” in ji Albanese. […]