Mutum Guda Ya Yi Shahada Sanadiyar Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen yakin HKI suka cilla a kan motarsa a kauyen Sair cikin lardin Nabadiyya.

Tashar talabijin ta Al-mayaddeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, sojojin yahudawan sun jefa boma-bomai har guda hudu a kan garin Kafar Kila a kudancin kasar ta Lebanon.

Labarin ya kara da cewa a garin kafar kila, sojojin yahudawan sun kai hare hare da dama a yau Jumma’a bayan wadanda muka bayyana amma basu kai ga kashe ko raunata wani ba.

A jiya Alhamis ma jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hare hare a wurare da dama daga ciki har da garin kafar Kila, da kuma kauyen taba’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments