Mutum Guda Ya Yi Shahada Sanadiyar Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen yakin HKI suka cilla a kan motarsa a kauyen Sair cikin lardin Nabadiyya. Tashar talabijin ta Al-mayaddeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, sojojin yahudawan sun jefa boma-bomai har guda […]

Malasiya Ta Bukaci A Kori Isara’ila (HKI) Daga MDD

Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Muhammad Hassan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasashen masu rauni a duniya sun damu da […]

Iran: China Ta Zuba Jari A Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana A Bushar

Shugaban kamfanin rarraba wutan lantarki na kasar Iran ya bada sanarwan cewa kasar China ta zuba jari na kimanin dalar Amurka miliyon 70 a aikin samar da wutan lantarki mai karfin MW 200 wanda kamafanin SATBA yake ginawa a lardin Bushar na kudancin kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Gholam […]

MDD Ta Yi Tir Da Dirar Mikiyan Da Jamus Takewa Masu Goyon Bayan Falasdinawa

Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: […]

Majalisar dokokin Iran ta gabatar da kudirin ficewa daga NPT

Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar […]

Guterres: Dole ne a kawo karshen halin da ake ciki a Gaza

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kira mummunan halin da ake ciki a Gaza a matsayin abu mafi muni a wannan lokaci ta fsuakr mawuyacin hali da dan adam yake ciki. Yayin da yake magana da manema labarai a birnin New York a ranar Alhamis, Antonio Guterres ya bayyana yadda ake lalata tsarin abinci da […]

Pezeshkian: Alakar Iran, China Na Da Amfani Mai Yawa Ga Kasashen Biyu

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dangantaka tsakanin Iran da China na dauke da dabarun manufofi masu kyau Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasar Iran na da sha’awar gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana da kasar China, musamman a fannin raya dabarun kiyaye hanya, yana mai bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu […]

Araqchi: Matakin Gungun Kasashen Turai Kan Iran Lamari Ne Da Zai Dagula Al’amura

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Matakin da gungun kasashen Turai ke son dauka kan Iran yana dagula tsarin diflomasiyya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi la’akari da yadda kasashen Turai uku suka yi amfani da tsarin warware takaddamar da ba bisa ka’ida ba a karkashin tsarin hadin gwiwa na (JCPOA) […]

Ma’aikatar  Harkokin Wajen Iran Ta Mayar Da Martani Kan Kudurin Tawagar Turai

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani ga Tawagar Turai na kokarin dawo da takunkumi kan kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwa a matsayin martani ga sanarwar da Tawagar Tura ta yi wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da baya kan ka’ida dangane da kuduri mai lamba 2231. Ma’aikatar harkokin wajen […]

Guterres: Shirin Gwamantin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Wani Babban Hatsari Ne

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon Shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a birnin Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadi kan mummunan sakamakon matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata dauka na fadada ayyukan soji a birnin Gaza, yana mai yin Allah wadai da manufofin fadada gine-ginen […]