Rahotanni daka birnin berut sun bayyana cewa sojojin HKI Sun kaddamar da wani hari a kudancin labanon a kuma yayi sanadiyar mutuwar wani mutum guda a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi da aka rattaba hannu akai tun a shekara ta 2024.
Ma’aikatar lafiya da cibiyar bayar da taimakon gaggawa ta kasar labanon ta fitar da sanarwar cewa sojojin HKI sun kai hari kan wata mota a garin bint jubail dake kudancin labanon da hakan ya kai ga shahadar wani dan kasar labanon guda daya.
Sojojin isara’ila daga baya sun sanar a shafinsu na X cewa sun kai harin ne da nufin samun wani mamba a kungiyar Hizbullah dake kasar labanon, tun bayan da aka kulla yarjejeniyar bude wuta isra’ila ta kashe daruruwan yan kasar labanon a hare haren da take kai wa a kasar,
Bisa yarjejeniyar da aka cimma isra’ila za ta kwashe sojojinta baki daya daga kudancin labanon a watan janeru amma har yanzu ta janye wasu kadan daga cikinsu ne amma ta ci gaba da kasancewa a sauran iyakokin kasar guda 5.